<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Ga alkawari na Allah cikin Littafi Mai Tsarki
 Yesu ya yi mani shi
 In kun roƙi kome ne. A cikin sunana dai-dai
 Shi zai ji addu'arka.

[V2]
 KORUS
 Yesu yana jiranmu mu zo gareshi
 Kome ya ke damunka
 Tashi dai ka yi addu'a
 Wanda ya zo gunsa, za a taimake shi,
 Lalle yana jin addu'a.

[V3]
 2) Dukan inda biyu ko uku suna nan a tattare
 Nan ya ke a tsakiya
 Dukan wanda ya yi roƙo tare da bangiskiya
 Za a ji addu'arsa.
 Korus

[V4]
 3) In na kiyaye mugunta a cikin zuciyata
 Allah ba zai ji ni ba,
 Addu'ar mai ƙin shari'a abin ƙyama ne ya ce,
 Allah ba zai ji ta ba.
 Korus

[V5]
 4) Bari dai mu yi addu'a kullum ba da fasawa
 Domin duka tsarkaka,
 Mu yi tsaro fa a ciki, mu yi tare da godiya
 Allah yana jin addu'a.
 Korus</lyrics>
<title>Ga Alkawari na Allah Cikin Littafi Mai Tsarki LW408</title>
<hymn_number>408</hymn_number>
</song>